Wakar gyara kayanka

Na Alhaji Dahiru Musa Jahun

 GYARA KAYANKA (BAKANSAMIYA)


Bismillahir Rahmanir Rahim, Wabihi nasta inu
1.     Gyara kayanka tsarin mutan kirki
Tai kira don a inganta tarbiyya
2.     Gyara kayanka ta ce gaisheku
Yan jihar Bauchi Gyara ake niyya
3.     Gyara kayanka ‘yar gomnatin Mallam
Mai adalci da kauna da soyayya
4.     Gyara kayanka ta shafi kowanmu
Babu gyara mafi gyara tarbiyya
5.     Gyara kayanka tsarin kwararru ne
Mai da jagora gubin farar hanya
6.     Gyara kayanka zancen masoyi ne
Mai gudun kar a fada abin kunya
7.     Gyara kayanka domin biranen mu
Gyara kayanka don kauyuka dinmu
Gyara kayanka don karkara tamu
Gyara kayanka ta shafi manyanmu
Gyara kayanka ta shafi yaranmu
Gyara kayanka ta shafi matanmu
Gyara kaya mazaje da matan me
Don hadin kai mu inganta kayanmu
          Sai da kishi da inganta tarbiyya.
8.     Gyara kayanka don masu yin mulki
Kuka jagora domin sanin hanya
9.     Gyara kayanka domin sanin hakki
Mai rikon gaskiya bai shiga kunya
10.                        Gyara kayanka amana ta al’umma
Rayuwa, dukiya, lafiya jinya
11.                        Gyara kayanka inganta alheri
Shugabancin kwarai kan farar hanya
12.                        Gyara kayanka domin gudun sharri
Duniya, lahira kar a sha kunya
13.                        Gyara kayanka tsarin tunashemu
Don hadin kai na kirki da soyayya
14.                        Gyara kayanka don yunkurin kirki
Shugabannin siyasar bidar mulki
Ko kasa ko jiha ko dukan yanki
Mai shirin yi da kai wanda ke mulki
Har zuwa shugabannin wajen aiki
Ko na’yankasuwa wane hamshaki
Ko sarakai da ma hakiman yanki
Gunduma unguwa littafan mulki
          Gyara kayanku inganta tarbiya.
15.                        Gyara kayanka gun malamai shine
Ai kiran gaskiya kan farar hanya
16.                        Gyara kayanka don yada addini
Kyauta suka da inganta jayayya
17.                        Gyara kayanka inganta imani
Sai farilla da sunna da tarbiya
18.                        Gyara kayanka don karku bacce mu
Kaico jagora in ya sake hanya
19.                        Gyara kaya makafi a hannun ka
In ka cuce su karshe kasha kunya
20.                        Fauka kulli zi ilmin alimun ne
Gyara kayanka don kauce hamaiya
21.                        Gyara kayanka kan malaman ilmu
Malaman zamani ko kwararru
malaman zamani ko kwararrun mu
Masu koyar da wayo ma junan mu
Masu ilmin fasahar sana’ummu
Ga amana a koyar da yaran mu
Kan tafarki na kirki su gaje mu
Dalibai ko ku dage bidar ilmu
Ci gaban zamani daukakar ilmu
          Gyara kayanka don gyara tarbiya
22.                        Gyara kayanka kan malaman ilmu
kar a koyar ma yara rashin kunya
23.                        Lakcaran jami’a ko muce tica
munyi fatan a inganta arbiya
24.                        Don sifofi dabiun wadansunku
kan gwada basu daidai da tarbiya
25.                        Tunda yara su kan dau sifar Mallam
bar fitowa da siffar rashin kunya
26.                        Gyara kaya iyaye ga ‘yayan su
Gyara yara su taso da tarbiya
27.                        Gyara kayanku ku malaman hadda
Maluman Tsangaya masu jan aya
28.                        Gyara Almajirai kare kur’ani
Kara inganta hanya mafi hanya
29.                        Gyara kayanka pasto batun coci
Masu bi karsu fada abin kunya
30.                        Gyara kayan kirista masoya ne
To maso gaskiya sai da tarbiya
31.                        Gyara kayan makwabci zumunta ce
Daina gaba da juna abin kunya
32.                        Gyara kayanku mata iyayen mu
Kuda ‘yayanku mata da matan mu
Gyara da’ar ku dai dai dabi’ummu
Gya kayanka domin matasan mu
Don rashin hankali ko rashin ilmu
Har su zam masu banga wa junan mu
Daina wauta da shirme magadun mu
Kui sana’u ku dage bidar ilmu
Gyara kayanku da’a da tarbiya
33.                        Nakkasassu a inganta imani
Gyara kayanka dai dai da tarbiya
34.                        Tun da safe bara har dare Mallam
Wassu kan je wuraren rashin kunya
35.                        Gyara kaya ta neman abincin ku
Rabbu ke ba sahihi da mai jinya
36.                        Masu halin sana’a su dan daure
Shawarar Gyara kaya ga mai niyya
37.                        Gyara kaya hukuma taana himma
Taimakon nakassasu da an shirya
38.                        Gyara kayanka ‘yan kasuwan kirki
Ga shirin kara jari akan hanya
39.                        Gyara kaya hadin kai na alheri
Don bidar arziki kan farar hanya
40.                        Gyara kayanka gwamnan mu yaji ku
Yayi fatan hadin kai tsakanin ku
Don shirin cimma burin bukatunku
Har dukan ‘yan sana’u makwabtan ku
Masu son kai ku inganta halin ku
Masu kishin kasa an fahimce ku
Ci gaban duk jiha ne ya dame ku
Kungiyoyin sana’u da sauran ku
Gyara kaya da inganta tarbiya
41.                        Gyara kayanka ‘yan kadago ance
ko na LG jiha ko na tarayya
42.                        Sai kulawa da aiki da makishi
kara inganta da’a tarbiyya
43.                        Kungiyar kodago tun kananun ku
hard a manya su dokta dama lauya
44.                        Gyara kayanka himma da ma kishi
Don hadin kai na da’a da tarbiyya
45.                        Kake, babur dfa mota ga mai tuku
Bangaren kai da kawo akan hanya
46.                        Hattara hankali ka’idar tuki
Gyara kayanka kafin shiga hanya
47.                        Tun da sauri ka haifar nawa Mallam
An karo an mace wassu na jinya
48.                        Allah kare batun Gyara kayanka
Kyan matuki da da’a da tarbiyya
49.                        ‘yan acaba ku inganta halin ku
mai bidar arziki bai rashin kunya
50.                        Kara inganta tsarin sana’arku
Gyara kayanka da’a da tarbiyya
51.                        Don wadansunku kan sa a zarge ku
Ga rashin hankali ga rashin kunya
52.                        In ya zam zaku gyara muna murna
Gyara kaya shirin gyara tarbiyya
53.                        Masu tuki na mota wadansu
Kan gwada ba mutunci bare kunya
54.                        Sai gdu ba kula babu bin oda
gyara kayanka don ka’idar hanya
55.                        Har way au dai kiran gyara kayanka
Ya mutane birane da kauyika
Muihadin kai akan ci gaban harka
Don zaman gaskiya wanda ba shakka
Kasuwa ko gida gun sana’arka
Gyara kaya da hakkin makwabcinka
Kar ka junan ki ko kai da junan ka
Ai zaman lafiya Gyara kayanka
Sai Mutunci da kauna da soyayya
56.                        Gwamnatin Bauchi Gwamna na adalci
Mai mutunci da kunya da tarbiyya
57.                        Gyara kayanka duk wanda ke aiki
anfi son mai amana da tarbiya
58.                        Gyara kayanka tsarin mutan kirki
don shirin farfadowa da tarbiya
59.                        Masu kayanka duk wanda ke aiki
an fi son mai amana da tarbiya
60.                        Yau jihar Bauchi Mallam yake Gwamna
bamu kaunar da’a da tarbiyya
61.                        Gyara kayanka dai wanda ka bata
Don hadewa cikin masu tarbiyya
62.                        Gyara kayanka tsari na adalci
Gyara halin mutane ake niyya
63.                        Gyara kayanka ba tsokana ce ba
Ba shiri ne na zargin mutane ba
Wanda bai gyara aikin shi sosai ba
Ba yakan gyara aikin mutane ba
Wanda bai gyara aikin shi sosai ba
Ba yakan gyara aikin mutane ba
Wanda bai san darajar mutane ba
To darajar shi ce bat a sosai ba
Wanda ko bai yi murna ta gyara ba
Ya gwada shi ba zai daina barna ba
Gyara kaya mu inganta tarbiyya
64.                        Gyara kayanka ko gyara kayanmu
Don hadewa mu inganta tarbiyya
65.                        Karka hau naka hangen na wassunmu
Gyara kaya shirin gyara tarbiyya
66.                        Gyara kayanka bai zam da laifi ba
Gun mutanen kwarai masu tarbiyya
67.                        Gyara kayanka kowa da laifinsa
Mai rikon gaskiya bai shiga kunya
68.                        Masu aikin tsaro gyara kayanku
Kare oda da doka da tarbiyya
69.                        Wane kayan hukuma kamar naka
Sai tsagerun abokai na ganganka
Sai gwanayen zuga ko kawalanka
Hart a buya kake kar a same ka
Kar mutane na kirki su dame ka
Shawari ka ki ka toshe kunnenka
Sa ido ofishin inda hotonka
To akwai hotunan wanda sun fika
Gyara kayanka da’a da tarbiyya
70.                        Masu aikin hukuma a gaishe ku
gyara kayanku inganta tarbiyya
71.                        Ga amana na aiki a gaishe ku
Mai rikon gaskiya bai shiga kunya
72.                        Gyara kayanmu dukkan mutan kirki
Don gujewa tafarkin abin kunya
73.                        Tsaftace zuciya tsaftace aiki
Gyara kayanka inganta tarbiya
74.                        Gyara kayanmu inganta halinmu
Kara inganta tsaftar farar hanya
75.                        Gyara kayanka tsafta cikin ofis
Har gidaje da gonad a kan hanya
76.                        Tsaftace kasuwa tsaftace shago
Tsaftace gun sana’a da tarbiyya
77.                        Sai hukuma ta tsafta a gaishe ku
Gyara kayanku birni da alkarya
78.                        Magudanan ruwa kun bi kun gyara
Hard a ma gefe-gefen jikin hanya
79.                        Kun yi himmar da tsafta ta inganta
Tun da kun share birni da alkarya
80.                        Sai anan ga tunin gyara kayanka
Mun yi murna da tsaftar bigen hanya
81.                        Ammana lunguna kan akwai bola
Ba’a kwasansu harma abin kunya
82.                        Masu tallan rake ko rowan leda
Munyi fatan ku inganta tarbiyya
83.                        Tun da leda da bawon rake din nan
Kan zamo datti gonad a kan hanya
84.                        Gyara kayanka don sanya inganci
Don kiran gaskiya mai muhimmanci
Mu da ku hard a su babu banbanci
Daina algus da kauce ma ha’inci
Ko matasa dake yada shashanci
Ko batun damfara ko na bokanci
Shaye-shaye na kwaya da iskanci
Ko gidan nuna kallo na fajirci
Daina wannan mu inganta tarbiyya
85.                        Gyara kaya tuni ne ga matan mu
Kar fada tafarkin rashin kunya
86.                        Ku iyayenmu mata da matanmu
Hard a ‘yayanmu mata asa niyya
87.                        Kara inganta hanyar abin kirki
Don gujewa ma hanyar shiga kunya
88.                        Masu aure ku dai kama aurenku
Sanya ‘ya’yaku mata farar hanya
89.                        Wassu gun talla da’a takan rushe
Har su koyo dabi’un rashin kunya
90.                        Gyara kayanka dai gyara kayanki
Don kira ce ta inganta tarbiyya
91.                        Sai da magunguna said a ilminsa
Gyara kaya cikin ayyukan jinya
92.                        Masu aiki na jinya wadansunku
Bas u jin tausayin wanda ke jinya
93.                        Gyara kayanka ko gyara kayanku
Masu aiki na jinya a gaishe ku
Sai ku inganta gyaran wadansunku
Don hadin kai na gyaran sana’arku
Su ka laifi ana bata sunanku
Ga kyamis ko ina sun wakilce ku
Said a magunguna babu yardarku
Ku na gargajiya mun tunashe ku
Gyara kaya batun ayyukan jinya

Tammat bi hamdillahi. Wasallallahu alan nabiyyil karim, wa ala alihi wa sahbihi wa sallam.



Daga Abdulhadi Abba Kyari 
Share on Google Plus

About Unknown

0 comments:

Post a Comment